Yau Ake Bikin Ranar Radiyo Ta Duniya

91

Yau ce Ranar Radio ta Duniya, kuma rana ce da aka kebe don duba tasirin Radio wajen inganta rayuwar jama’a.

A shekara ta 2011 ne kungiyar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ilmi da al’adu, watau UNESCO, ta kebe kowace ranar 13 ga wata Fabarairu a zaman Ranar Radiyo ta Duniya.

A cewar kungiyar UNESCO, radio na kan gaba a matsayin hanyar sadarwa ga al’umma mai yawa a ko’ina a duniya, a kuma cikin lokaci kankani.

Bikin dai na kokarin janyo hankulan jama’a ne kan tasirin rediyo wadda ta zama kafa mafi kai wa ga dumbin mutane kuma a yanzu take daukar sabbin siffofin fasahar zamani

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan