Tsohon Sanatan mazabar kudancin jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya bayyana murnar kammala digirinsa na biyu, wanda ya kammala a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Sanata Dino Melaye, ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk, inda ya ce yana taya kansa murnar kammala digiri na biyu a karo na shida.
“Ina taya kaina murnar kammala digirina biyu a karo na shida”


Ko a cikin watan Maris na shekarar 2017 sai da Dino Melaye ya tabbatarwa da duniya cewa yana da digirin farko guda takwas.
Turawa Abokai