Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Ya Yi Sababbin Naɗe-naɗe

106

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da naɗin mataimaka na musamman a cikin kunshin gwamnatinsa.

Tun da farko an raba takardun kama aiki a ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji.

Wadanda aka naɗa ɗin su ne:


Comrade Aliyu Mai Kasuwa Muhammad, mataimaki na musamman akan harkokin ƙungiyoyin ɗalibai.

Bashir Barwan Yola, mataimaki na musamman akan ƙidaya.

Ado Abdullahi Tati, mataimaki na musamman akan harkokin ɗalibai.

Adamu Mukhtar Musa, mataimaki na musamman akan harkokin matasa.

Dr Hussain Jarma, mataimaki na musamman akan harkokin Ilimi mai zurfi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan