Wasu Mata Biyar Sun Mutu Sakamakon Ruftawar Ƙasa A Kano

100

Wannan al’amari ya faru ne a jiya Alhamis a cikin kauyen Dauni dake karamar hukumar Minjibir da ke jihar Kano, inda wadannan mata suka rasa rayukan su a lokacin da suke tsaka da diban kasa a cikin wani rami.

Wadanda abun ya faru a gabansu sun bayyana cewa matan suna tsaka da tonon kasar ne sai kasa ta rubta musu ta binnesu a ciki.

Mazauna wannan yanki sun bayyana cewa dama matan kauyen sun dade suna diban wannan kasa suna kaiwa kasuwar kofar Wambai dake cikin birnin Kano suna siyarwa.

Tuni dai akayi jana’izar wadannan mata aka kai su makwancin su, yayin da shi kuma yaron daya jikkata wanda akace dan shekaru Biyar ne wanda aka zakulo da ransa ba’a bayyana cewa an kaishi asibiti ba ko kuma a’a.

Mazauna wannan yanki na Dauni basu bayyana takamaimai abinda akeyi da wannan kasa ba da mata ke tonon ta suna kaiwa kasuwa suna siyarwa,saidai wasu sunce ana amfani da ita ne wajen yin hodar mata ta kwalliya.

Jami’in yada labarai na karamar hukumar ta Minjibir Tasi’u Dadin Duniya da kuma takwaran sa na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Sa’idu Muhammed Ibrahim sun tabbatar da aukuwar wannan lamari saidai basuyi wani karin bayani ba akai.

Jaridar Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan