Matukar Ina Kan Mulki Babu Wanda Ya Isa Yayi Auren Jinsi A Ƙasar Rasha – Putin

11

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yaki yarda ya rattaba hannu akan dokar da za ta bayar da damar yin auren jinsi a kasar.

Da yake magana a ranar Alhamis a Kremlin, inda ya gana da kwamishinan jihar domin su yi magana akan canjin kundin tsarin mulki na kasar Rasha, shugaban kasar mai shekaru 67 ya bayyana cewa ba zai bari a bata al’adar da suka ta so da ita tun iyaye da kakanni ba.

“Na riga na yanke hukunci akan wannan maganar, kuma zan sake fada ma yanzu, matukar nine akan mulki babu wanda ya isa yayi auren jinsi a kasar nan.” Cewar Putin.

A watan da ya gabata ne firaministan kasar Dmitry Medvedev, da sauran manyan gwamnatin kasar suka yi murabus, bayan shugaban kasar ya gabatar da wata doka da za ta bashi damar cigaba da mulki har abada.

Da yake magana da ‘yan majalisarsa a wannan lokacin, Putin ya gabatar da dokar da za ta karawa ‘yan majalisun kasar damar jimawa akan mulki.

“Nayi nazari akan bawa ‘yan kasa damar kada kuri’a akan dokar da za ta kawo canji akan kundin tsarin mulkin kasar nan,” Putin ya ce.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan