Gobara Ta Hallaka Yara 15 A Wani Gidan Marayu

73

Gobara ta kashe yara guda 15 a wani gidan marayu bayan tashin wutar da tsakar dare a lokacin da yaran ke barci a kasar Haiti.

Yara fiye da 60 ne ke barci a gidan marayun sadda gobarar ta tashi, a cewar shugabar cibiyar kula da jin dadin jama’ar kasar Haiti, Arielle Jeanty Villedrouin.

Gwamnatin Haiti ta ce yara biyu ne wutar gobarar ta kashe yayin da sauran 13 suka mutu a asibiti saboda shakar hayakin da ya turnike su a gobarar.

Gidan marayun mallakar wani cocin mishinare daga Amurka a Haiti na daga cikin daruruwan ire-irensa da ke aiki ba bisa ka’ida ba kasar tun daga shekarar 2013.

Hukumomi ba su kai ga gano musabbabin gobarar ba, amma rahotanni na cewa jami’ai da yara da ke gidan marayun sun koma kunna kendira saboda rashin wutar lantarki.

Arielle ta ce gwamnatin kasar na kokarin sama wa sauran marayun da suka tsallaka rijiya da baya wani matsuguni.

Ta kara da cewa za a gudanar da bincike domin gano dangin yaran domin sake mayar da su ga iyalensu.

Gwamantin kasar ta ce gidan marayun ya kasa samun rijista ne saboda rashin cika ka’idoji da kuma yadda yake barin yara cikin mawuyacin hali.

Akalla yara 30,000 ne ke zaune gidajen marayu 760 da ke kasar, wadanda kashi 15 daga cikinsu ne kawai ke da rijista, a cewar kungiyar jin kai ta Lumos, da ke aiki a kasar.

Kungiyar mai suna Church of Bible Understanding ta ce ta shafe sama da shekara 40 tana aiki a Haiti, kuma babban aikinta a kasar yada da’awar masihiyya a kasar Haiti.

Har yanzu kungiyar ba ta ce uffan a kan gobar ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan