Matan Saudiya Sun Fara Busa Sigari A Fili Da Sunan Ƴanci Da Wayewa

46

A yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, daya daga cikin matan Saudiya mai suna Rima ‘yar shekaru 17 da ke aiki a wani kamfani na birnin Riyadh, ta ce, busa sigari a bainar jama’a na cikin ‘yancinta da ta samu a baya-bayan nan.


Rima wadda ta fara zukar sigari shekaru biyu da suka gabata, ta yi watsi da illar da tabar ke yi wa lafiyar bil’adama, amma ta nuna cewa, ba ta son danginta su gano cewa tana shan taba.


Ko da yake ta ce, a shirye take ta kare kanta a gaban dangin nata saboda mata na da ‘yancin shan sigari kamar takwarorinsu maza.

Masharhanta na danganta hakan da tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa ciki har da bai wa matan ‘yanci da Yarima mai jiran gado Muhammed Bin Salman ke aiwatarwa.


A halin yanzu mata na da ‘yancin tuki da kansu, da halartar filayen wasanni da bukukuwan kalankuwa, da kuma damar yin tafiye-tafiye ba tare da muharraminsu ba, abubuwan da a shekarun baya aka haramta musu

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan