Ɗimbin Albashin Da Ake Biyan ‘Yan Majalisa Daidai Ne- Buhari

120

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kuskure ne ‘yan Najeriya su riƙa ɗauka cewa ɗimbin albashin da ake biyan ‘yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ya yi yawa, kuma aikin da suke yi bai taka kara ya karya ba.

Ya ce rashin amincewa da ‘yan majalisa ya sa masu sukar su sun kasa ganin ɗimbin ayyukan da suke yi wa ƙasar nan.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ranar Laraba a Abuja lokacin da Majalisar Wakilai ta ƙaddamar da wata mujalla mai suna ‘The Green Chamber Magazine’ wadda Kwamitin Majalisar na Kafafen Watsa Labarai da Huɗda da Jama’a ya samar.

Taron ƙaddamar da mujallar ya samu halartar Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, wanda ya wakilci Shugaba Buhari; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Ovie Omo-Agege, wanda ya wakilci Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan; gwamnan jihar Katsina kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Aminu Bello Masari da gwamnan jihar Imo kuma tsohon sanata, Hope Uzodinma.

Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da Mataimakin Kakakin Majalisar, Ahmed Wase su suka jagoranci shugabannin majalisar da kuma sauran mambobin majalisar zuwa taron.

Shugaba Buhari, wanda ya yi jawabi ta bakin Mista Mohammed, ya ce ‘yan majalisa ba sa raba kuɗi ba tare da sun yi aiki ba.

“A yanzu, abinda ake ɗaukar Majalisar Dokoki ta Ƙasa shi ne tana da ɓangare biyu dukkan ‘yan majalisa da majalisa da suka cancanta suke samun ɗimbin kuɗaɗe a aljihunsu bisa aikin da bai taka kara ya karya ba. Wannan tunani ya samu ne sakamakon rashin fahimtar tarin aikin ‘yan majalisar, musamman a wajen kyamarar talabijin.

“Amma da samun wata mujalla da za ta zama wata sahihiyar majiya ta duk abinda ke gudana a Majalisar- ƙudurorin da ake gabatarwa, dokokin da ake zartarwa da al’amuran ƙasa da ake tattaunawa da ayyukan mazaɓu, al’umma za su samu bayanai sosai bisa aikace-aikacen Majalisar, wannan kuma zai haifar da kyakkyawar fahimtar al’umma ga majalisar.

“Bugu da ƙari, mujallar za ta taimaka wa Majalisar ta bada labarin kanta da kanta, maimakon dogara da wasu su bayar da labarinta. Ana cewa ba wanda zai iya bada labarinka fiye da kai”, in ji Shugaba Buhari.

Tsohon Daraktan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci ta Kenya kuma Daraktan Makarantar Nazarin Shari’a ta Kenya, Farfesa Plo Lubumba, wanda ya kasance babban mai jawabi a yayin taron ya tamabaya don jin ko ‘yan majalisar suna bin sahun waɗanda suka kafa Najeriya, waɗanda ya ce suna da kyakkyawan shiri ga Najeriya.

“Na karanta tarihin manyan shuagabanninku da suka kafa Najeriya. Na karanta irin aikace-aikacen Nnamdi Azikiwe kuma na saurare shi a wancan lokaci. Yana da fasahar harshe saboda yadda yake sha’awar yi wa ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Afirka jawabi, saboda haka aka kira shi da Zik na Afirka- wancan shugabanci da suka yi ya tafi ne kan yi wa jama’a hidima. Za ku iya amfani da wannan mujalla wajen nuna wa Afirka cewa ku shugabanni ne masu yi wa jama’a hidima”, in ji Mista Lubumba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan