Gidauniyar Atiku Za Ta Horar Da Matasa 2000 Yadda Ake Rubuta JAMB A Maiduguri

197

Shugaban gidauniyar ‘Atiku Care Foundation’ na kasa reshen jihar Borno, Honarabul Ibrahim Ali Amsami, ya bayyan cewa gidauniyar sa za ta horar da matasa maza da mata mutum dubu biyu (2,000) wadanda za su rubuta jarabawar shiga jami’a wato JAMB, domin sanin yadda matasan za su sarrafa Kwamfuta wajen rubuta jarabawar.

Ibrahim Amsami, ya bada wannan tabbaci ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a babban birnin jihar Borno.

“Za mu ɗakko matasa 74 daga kowacce ƙaramar hukuma a jihar Borno, domin horar da su yadda za su rubuta jarabawar JAMB a Kwamfuta”


Ya kara da cewa wannan yana cikin kudurin gidauniyarsu na ganin sun magance irin matsalolin da ake samu a lokacin rubuta jarrabawar ta JAMB.

A ƙarshe Honarabul Ibrahim Amsami, ya yi kira ga mahukunta da su mayar da hankali wajen bunkasa ilimi a fannoni daban-daban domin samun zaman lafiya mai daorewa da karuwar arziki a fadin kasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan