Inganta Rayuwar Marayu Da Marasa Ƙarfi Shi Ne Burina – Rabi Yusuf Gwamna

243

Shugabar Gidauniyar Rabi Gwamna da ke tallafawa marayu da marasa galihu a jihar Kano, Hajiya Rabi Yusuf Gwamna, ta yi kira ga al’umma masu hannu da shuni da su taimaka wajen inganta rayuwar marayu da marasa gata da ke rayuwa a fadin jihar Kano.

Rabi Gwamna ta yi wannan kiran ne a lokacin da ta ziyarci ofishin Labarai24.

“Hakika akwai bukatar masu kudi da su bayar da gudummawa wajen inganta rayuwar marayu da marasa galihu”

“Wannan gidauniya tamu ta Rabi Gwamna, muna bakin kokarinmu wajen ganin mun tallafi rayuwar marayu da marasa, ta hanyar basu tallafi da kuma biya musu kudin makaranta”

Hakazalika, ta kara da cewa babban kalubalen da ta gidauniyar ta ta ke fuskanta shi ne rashin wanda zai ɗauki nauyin aiyukanta.

“La’akari da yadda mu ke kokarin inganta rayuwar marayu, muna bukatar waɗanda za su kara tallafawa aiyukan wannan gidauniya tamu mai albarka”

Ta bayyana babban makasudin wannan gidauniya shi ne taimakawa Marayu da Gajiyyayu da Marasa Gata ta Fannin Ilimi da Lafiya da kuma Inganta Rayuwar su, da dai sauran su.

Hajiya Rabi Yusuf ta ce sun samu nasarar ziyarar gidan marayu da ke Nasarawa, a jihar Kano, inda su ka samar da abinci da kuma kayan amfanin yau da kullum. Baya ga nan kuma sun biyawa wasu marasa galihu kudin makaranta a matakin jami’a, domin hakan zai inganta rayuwarsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan