Aiyukan Sabon Da Mu Ke Aikatawa Ne Ya Jawo Mana Matsalar Tsaro – Sultan

71

Matsalar tsaro dake addabar kasarmu yana daya daga cikin hukuncin da Allah yake mana na kin bin umarnin shi, cewar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III.

Da yake bayani a wajen taron kasa da kasa na biyar da aka gabatar kan “Soyayya da hakuri wajen wanzar da zaman lafiya da kuma rage wuce gona da iri,” wanda aka yi a Abuja.

Sarkin Musulman ya ce ‘yan Najeriya suna zaune cikin aikata zunubai, kuma sunki su bi dokokin da Qur’ani da Bible suka koyar.

Sarkin Musulman wanda ya samu wakilcin Sarkin Jiwa, Dr. Idris Musa, ya nuna damuwa kan yanayi na rashin tsaro a Najeriya. ya ce abin ya kai matsayin da masu kudi suna tsoron talakawa.

“Matsalar tsaro shine matsalar mu. Al-Qur’ani mai girma sako ne aka aikowa al’ummar duniya baki daya. Haka shi ma littafin Bible sako ne ga al’ummar duniya. Idan har baza mu yi aiki da abinda Qur’ani da Bible suka zo da shi ba, kuma muka cigaba da yin abinda muke so, tabbas irin wannan sakamakon ne ya cancanta a kanmu.

“Wannan yana daya daga cikin hukuncin da muke karba daga wajen ubangiji kan sabon da muke aikatawa. Idan har zamu daina aikata sabo, kuma muyi biyayya ga Allah tabbas komai zai canja.

“Ina godiya ga UFUK da kokarin da suke yi na ganin sun hada kan al’ummar duniya wajen sanya kaunar juna a ransu. A yanzu muna lokaci da bama kaunar junanmu ko kadan. Wannan ba daidai bane ko kadan. An halicce mu iri daya ne kuma mu ‘yan uwane.

“Muna rokon kowa da kowa dasu zo mu zauna lafiya. Ba zai yiwu mu dinga zaluntar junanmu ba,” ya ce.

Sarkin Musulman ya bayyana cewa Najeriya za ta kawo hanyar da za ta kawo karshen matsalar tsaro da take fama da ita.

“Zamu yi nasara a kan matsalar tsaro. Kowa yana jin tsoron kowa, amma na san cewa tabbas zamu kawo karshen wannan matsala. Yanzu mun zo lokaci da masu arziki suna gudun talakawa, saboda yana tunanin zai iya rasa ranshi.” cewar shi.

Yayi kira ga Musulmai da Kiristoci su cigaba da addu’ar Allah ya saukar mana da rahamarsa a Najeriya, ya kawo hadin kai a kasar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan