Hukumar EFCC Ta Damƙe Mukhtar Ishaq Yakasai Bisa Zargin Almundahana

171

Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati reshen jihar Kano, ta kama tsohon shugaban karamar hukumar birnin Kano da kewaye, kuma kwamishina aiyuka na musamman, Mukhtar Ishaq Yakasai.

Sanarwar kamun Mukhtar Ishaq Yakasai din na kunshe ne cikin wata takarda da kakakin hukumar Tony Orilade ya fitar.

Tun da farko an kama Mukhtar Ishaq Yakasai, bisa korafin da aka gabatar a gaban hukumar ta EFCC, akan zargin karkatar da wasu kudade da ya yi lokacin yana Shugabancin karamar hukumar birnin Kano da Kewaye.

Masu korafin sun bayyana yadda Mukhtar Ishaq Yakasai ya karkatar da makudan kudade da su kai naira miliyan 76, wanda aka ware domin aiyukan raya kasa.

Bugu da kari hukumar ta EFCC ta bayyana cewa masu korafin suna kuma zargin Mukhtar Yakasai da cirewa kansilolin karamar hukumar birnin Kano, naira dubu 30 ba tare da wani dalili ba.

Hakazalika, masu korafin sun yi zargin yadda Mukhtar Ishaq Yakasai ya sayar da filayen makarantar Furamaren kofar Nasarawa akan kudi naira miliyan 10 kowanne.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan