Kotu Ta Ɗaure Malamin Jami’a Shekaru 21 Saboda Laifin Fyaɗe

124

Wata babbar kotu da ke birnin Lagos ta yanke wa tsohon malamin jami’ar Lagos, UNILAG hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari saboda samun sa da laifin yi wa daliba mai shekaru 18 da ke neman gurbin karatu fyade.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa, Mai Shari’a Josephine Oyefeso ta bayyana fyaden da Akin Baruwa ya yi dalibar a matsayin mummunan laifi.

Mai Shari’ar ta yi fatan wannan hukuncin zai zama izina ga wasu, yayin da ta ce, malamin ya keta mutuncin matashiyar, abin da ka iya haifar mata da damuwar din-din-din a rayuwarta.

Abin kunya ne abin da malamin ya aika, in ji Oyefeso.

Rahotanni sun ce, malamin jami’ar ya kasance amini ga mahaifin dalibar, yayin da ya yi kokarin kare kansa a gaban kotu, inda ya ce, dalibar ce ta yaudare shi har ya yi lalata da ita a ofishinsa da ke jami’ar UNILAG.

Sai dai dalibar ta ce, ya yi amfani da karfi wajen lalata da ita, kuma shi ne mutun na farko da ya keta mata mutunci.

Ana yawan zargin malaman jami’o’in kasar nan da wasu kasashen Afrika da yi wa dalibai mata fyade da sunan taimaka musu samun makin cin jarabawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan