A Karon Farko An Samu Wani Mutum Yana Bautawa Donald Trump

100

Bussa Krishna, mai shelaru 37 da haihuwa dan kasar India ya ce shugaban kasar Amurka Donald Trump ne Ubangijinsa, kuma ya fara bauta masa ne tun a cikin shekaru hudu da suka gabata bayan ya gan shi a mafarki.

Bayan wannan mafarkin da ya yi, Krishna ya ce yayi hayar leburori 15 wadanda suka yi aikin gina gunkin mai tsayin kafafu 6 na Trump a kauyensu da ke Kudancin Telangana a India.

“A maimakon in fara bautar wani ubangiji, na fara bauta masa,” Bussa Krishna ya sanar da gidan talabijin na New Delhi, yayin nuna musu gunkin Trump da ke sanye da kaya na alfarma. Yana kiran gunkin da “Ubangijina, Donald Trump.”

“Kaunar da ke tsakanina da shi ta koma ta tsakanin Ubangiji da bawansa. Wannan na kara min farin ciki ba kadan ba. Amma kuma ina fuskantar kalubale daga ‘yan uwana,” in ji Krishna.

Tamkar Ubangiji yake gareni, hakan ne dalilin da yasa na gina gunkin sa. A kowacce ranar Juma’a ina azumi domin fatan tsawon rayuwa ga Trump. Ina duba hoton sa tare da yin addu’a gareshi kafin in fara aiyukana. Trump, kaine Ubangijina kuma ina maka barka da zuwa India. Ina matukar farin ciki.”

Krishna wanda yake rayuwar shi kadai, an san shi a yankin yanzu da Trump Krishna kuma ana kiran gidan sa da gidan Trump.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan