Akwai Yiwwuwar Sterling Yatafi Real Madrid

98

Akwai yiwwuwar dan wasan gefe na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City kuma dan asalin kasar Ingila wato Raheem Sterling yatafi kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Saidai da aka tambayi mai horas da kungiyar kwallon kafan ta Manchester City wato Pep Guardiola dangane da tafiyar Sterling sai yace “ni bani da matsala akan tattaunawarmu dashi don idan yace zaitafi bazan iya hanashi ba”

Tun a shekarar data gabata kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tafara tattauna neman Sterling.

Sterling dai yana daga cikin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City masu kwazo da hazaka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan