Mulkin Buhari Tamkar Ruwan Kogi Ne Da Ya Ke Kokarin Cinye Gari – Nazir Adam Salih

198

Fitaccen marubucin nan kuma mai rubuta fina-finai a masana’antar Kanywood, Nazir Adam Salih, ya bayyana cewa mulkin shugaba Muhammad Buhari, tamkar ruwan kogi ne da ya ke kokarin cinye gari.

Nazir Adam, ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk.

“Mulkin Buhari kamar ruwa ne ke kokarin cinye gari maimakon ka tare shi sai ka ballo teku! Allah ka taimaki Najeriye”

Al’ummar ƙasar nan na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu game da yadda shugaba Muhammadu Buhari ke tafiyar da gwamnatinsa.

Wasu suna yabon gwamnatin, yayin da wasu kuma ke cewa har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, musamman ga gwamnatin da aka zaba domin kawo sauyi a fadin kasar nan.

Sai dai wasu masana na ganin akwai babban kalubale a gaban shugaba Muhammadu Buhari ganin yadda wasu da dama ciki har da ‘yan jam’iyarsa suka dawo daga rakiyar gwamnatinsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan