Lampard Ya Shiga Tsaka Mai Wuya

95

Dan wasan Faransa, kuma zaƙaƙorin ɗan tsakiyar filin Chelsea wanda ya lashe Kofin Duniya ya yi raunin lokacin fafatawar da Manchester United ta doke su da ci 2-0 ranar Litinin da ta wuce.
Jinyar da zai yi babban koma-baya ne ga Chelsea, wacce za ta buga wasan lig shida da kuma cup games a mako ukun da ke tafe.
“Ya ji rauni a tsokarsa, irin wanda ya ji lokacin wasanmu,” in ji Lampard
Kante zai yi jinya ne a lokacin da Chelsea ke tsaka mai wuya a kakar wasa ta bana.

Chelsea za su fafata da Bayern Munich a wasan ‘yan 16 na gasar Zakarun Turai ranar Talata mai zuwa sannan su sake karawa a Jamus ranar 10 ga watan Maris.

Chelsea, wacce ita ce ta hudu a saman teburin Firimiya amma bata ci wasa a karawarta a wasa hudu mafi muhimmanci ba, ta gwabza da Tottenham a wasan hamayya a London a jiya ranar Asabar yadda ta lallasa makwabciyar tata da ci 2.1 a birnin London.

Kazalika, za su karbi bakwancin Liverpool a zagaye na biyar na gasar cin Kofin FA ranar uku ga watan Maris, yayin da za su fuskanci Bournemouth da Everton a gasar Firimiya a ranar 29 ga watan Fabrairu da takwas ga watan Maris.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan