Real Madrid Tayi Babu Tsuntsu Babu Tarko

77

Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid tayi babu tsuntsu babu tarko inda garin hangen buga gasar zakarun nahiyar turai yasa ta sakko daga jan ragamar teburin gasar Laliga.

Real Madrid din ta saukane bayan Levante tayimata saukalen kwallo 1 tilo mai ban haushi.

Wannan rashin nasara da Madrid tayi yasa magoya baya dama masu ruwa da tsaki na wannan kungiya sun shiga damuwa.

Yanzu dai Madrid sun dawo na 2 inda babbar abokiyar hamayyarsu ta hau teburin gasar wato Barcelona.

A mako mai zuwa ne za a fafata wasan hamayya mafi kyau a duniyar kwallon kafa tsakanin Real Madrid da Barcelona wasan da akayiwa lakabi da El-Classico.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan