Tarihi: Shekaru Huɗu Da Rasuwar Jaruma Aisha Dankano

221

Ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar 2016, Allah ya yi wa fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Aisha Dankano rasuwa.

Aisha wacce aka fi sani da Sima ta rasu ne bayan jinya ta makonni biyu a Kano.

Duk da cewa marigayiyar ta dan yi jinya na tsawon makonni biyu kafin rasuwarta amma hakan bai hana abokan sana’arta shiga rudani a daidai lokacin da suka samu labarin rasuwarta ba. A cewar mafi yawa daga cikinsu, ba su taba tunanin ciwon nata na ajali ba ne.

Kafin rasuwarta dai ta kasance daya daga cikin fitattun jaruman da ke fitowa a matsayin uwa, kuma ta shahara sosai a dandalin Kannywood.

An haifi marigayiya A’isha Dankano a unguwar Gwamamja, yankin karamar Hukumar Dala, Jihar Kano, kimanin shekaru 40 da suka gabata. Ta yi karatunta na firamare har zuwa sakandare a Kano, inda daga nan ta yi aure har ta haifi ’yarta daya. Bayan aurenta ya mutu ne ta shiga harkar fim din Hausa.

Marigayiyar ta shiga harkar fim ne shekaru 19 da suka wuce, inda ta fara fitowa a fim mai suna Bilkisu. Sai dai wani fim da ya fito da ita, shi ne fim din Sima. Haka kuma fim din da ta fito cikinsa na karshe, shi ne fim din kyalkyal Banza, wanda a karshe ma ba ta iya karasa shi ba, sakamkon ciwon da ya yi mata tsanani.

Marigayiyar ta fito a fina-finai masu yawan gaske, haka kuma ta samu kyaututtukan yabo daban-dabn, domin ta taba karbar kyautar MTN/Kannywood Award a matsayin jarumar da ta fi kowa kwarewa a iya shirya mugunta a fim.

Marigayiyar ta rasu ta bar mahaifiyarta da ke zaune a garin Sakkwato da kuma ’yarta budurwa wacce kwanaki goma suka rage a aurar da ita

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan