Ni Ɗan Kwankwasiyya Ne Ba Ɗan Jam’iyyar PDP Ba — Rufa’i Sani Hanga

213

Tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Rufa’i Sani Hanga, ya bayyana cewa shi ɗan Kwankwasiyya ne ba ɗan jam’iyyar PDP ba, kamar yadda wasu su ke yaɗawa.

Rufa’i Sani Hanga, wanda ya taba zawarcin kujerar sanatan Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC, a kakar zaɓen shekarar 2019.

Hakazalika kafin zaɓen shekarar 2019, Rufa’i Hanga, yana daga jigogin jam’iyyar APC a jihar Kano, sai dai kuma sun samu sabanin siyasa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan muradinsa na ganin ya samu takarar sanatan Kano ta tsakiya, wanda hakan ne ya sanya ake ganin fuskarsa a tarukan ƴan Kwankwasiyya tare da kare manufofin sanata Rabi’u Kwankwaso.

Tun da farko dai an gano fuskar Sanata Rufa’i Hanga tare da madugun ɗarikar Kwankwasiyya, a shalkwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, wanda hakan ne ya haifar da jita-jitar tsohon Sanatan ya koma jam’iyyar PDP.

Rufa’i Sani Hanga ya ce ya ga abubuwan cigaba a tattare da Sanata Rabi’u Kwankwaso da kuma Kwankwasiyya.

“A lokutan baya ina ƙalubalantar Kwankwaso ne, amma bayan ganin gaskiyarsa da nagartarsa sai ya sanya na aminta cewa tafiyar Kwankwasiyya, tafiya ce ta mutane masu nagarta da daraja”

“Ina kallon Sanata Kwankwaso a matsayin shugaba mai nagarta da hangen nesa, wanda hakan ya sanya idan ya bukaceni da in koma jam’iyyar PDP ko kuma wata jam’iyyar, babu shakka zan shiga”

A ƙarshe Sanata Rufa’i Sani Hanga, ya ce yana tare da Rabi’u Kwankwaso, saboda yadda da manufofinsa na cigaban al’umma, haka kuma ya ce su a har kullum suna kan akida ne ba wai jam’iyyar siyasa ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan