A Karon Farko Ƙasar Ireland Ta Yi bikin Murnar Auren Jinsi

128

A Jamhuriyar Ireland, Dubun bubatan jama’a ne suka mamaye titunan Dublin, babban birnin Kasar inda suka gudanar da gagarumin bikin nuna farin ciki da kuma alfahari cewa Kasar ce ta farko a duniya da ta fara kada kuri’ar raba gardama akan auren jinsi guda.

Kimanin kashi 62 cikin 100 ne na al-ummar kasar suka goyi bayan yin auren jinsi gudan a kuri’ar.

Wannan na zuwa ne bayan Kotun kolin Amurka ta halatta auren jinsi guda a jihohi hamsin na Kasar.

A bangare guda, wasu ‘yan kasashen kudancin Amurka da su ka hada da Chile da Mexico sun yi pareti, inda suka bukaci hukumomi da su basu cikakken ‘yancin auren jinsi kamar yadda kasar Amurka ta yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan