Ganduje Ya Haramta Barace-Barace A Kano

9

A ƙoƙarin tabbatar da nasarar shirin ilimi kyauta kuma wajibi a jihar Kano, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya haramta barace-baracen almajirai a titunan Kano.

Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Talata a yayin ƙaddamar da wani shiri mai taken Basic Education Service Delivery for All, BESDA, da kuma raba takardun ɗaukar aiki ga malaman wucin gadi 7, 500, kamar yadda yake a ƙunshe a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Ganduje, Abba Anwar ya fitar.

A cewar Gwamna Ganduje, shigar da tsarin almajiranci a cikin na boko zai yi maganin barace-baracen almajiran da ta daɗe tana ci wa jihar tuwo a ƙwarya.

“Wannan shiri na ilimi kyauta kuma wajibi yana tare da shigar da tsarinmu almajiranci zuwa aiwatar da wannan babbar manufa wadda ta bada shawarar cewa a shigar da koyar da Turanci da Lissafi a manhajar makarantun almajirai.

“… yayinda za su (almajirai) ci gaba da karatun Ƙur’ani, a lokaci guda kuma za su riƙa koyon Turanci da Lissafi, wannan zai ba su dama su ci gaba da karatu zuwa sakandire har ma gaba da sakandire”, in ji shi.

Gwamna Ganduje ya ce za a tura waɗannan malamai 7,500 zuwa makarantun Islamiyya da na almajirai “don a shigar da makarantunmu na almajirai a ƙarƙashin sabon shirinmu na ilimi”.

Saboda haka ne Gwmana Ganduje ya gargaɗi malaman almajirai waɗanda ba za su yi biyayya ga wannan sabon tsarin makaranta ba, yana mai jaddada cewa: “Idan kana tunanin ba za ka karɓi wannan tsarin ba, to ka bar jihar nan”!.

Shi ma a nasa jawabin, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano a ɓangaren ilimi, yana mai cewa abinda Kano ke yi a ƙarƙashin wannan sabon shirin abin koyi ne.

Mista Adamu ya samu wakilcin Daraktar Ma’aikatar Ilimi ne, Misis Liman.

A nasa tsokacin, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano, SUPEB, Dakta Danlami Hayyo ya bayyana cewa banda gina sabbin azuzuwa da yi wa da yawa kwaskwarima, gwamnatin jihar Kano ta kuma samar da kujeru masu cin mutum uku guda 16,327 a makarantu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan