Hukumar Hisbah Ta Samu Wata Bazawara Da Ta Ke Auren Maza Biyu A Kano

331

Matar mai suna Hauwa kulu mazauniyar unguwar Mariri tana zaune da mijinta na farko mai suna Bello sai rashin lafiya ta same shi ita kuma ta saka shi a mota ta aike dashi garinsu.

Daga bisani kuma ta dawo ta cigaba da zamanta, shi kuma Yana can Yana jinya sai mijin data aura na biyu ya gamu da ita ta kuma shaida masa ita bazawarace, inda nan take ya zare kudinsa har Naira dubu Ashirin ya biya sadaki.

Da ya ke direbane ya hau motarsa ya tafi nema, daga bisani takirashi tace dashi an daura musu aure lokacin da ya dawo gidansa dakin amarya suna soyewa, sai mijin Farko ya bayyana ko da zuwansa sai ya gamu da wani mutum a cikin dakinsa nan da nan ya kwarma ihu, shi kuma mijin na biyu yace yana tuhumarsa da shigar masa gida batare da izini ba.

Nan da nan rikici ya kaure har zuwa ofishin hukumar Hisba da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso.

A nata bangare wannan mata mai auren maza biyu ta bayyana cewa ai mijin farko wato Bello ya sawwakemata inda shi kuma yace wannan magana ba dashi aka yi taba.

Malam Bala shi ne mijinta na biyu yace shifa matarsace kuma babu Wanda zai rabashi da ita Tunda yanzu ma harta haifa masa yaro guda duk da yake a can baya suna da yara shida da tsohon mijin nata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan