Kotu Ta Bada Umarnin A Ƙyale El-zakzaky Da Matarsa Su Ga Likita

91

A ranar Litinin ne Babbar Kotun Jihar Kaduna ta umarci Babban Gidan Gyaran Hali na Kaduna da ya ba Ibrahim El-zakzaky, Shugaban Ƙungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Najeriya, IMN, wadda aka fi sani da Shi’a da matarsa, Zeenat damar ganin likita kafin su mayar da martani game da ƙarar da aka shigar da su ranar 23 ga watan Afrilu.

Kotun, wadda Mai Shari’a Gideon Kurada ya jagoranci zamanta, ta bada umarnin ne bayan Kwanturolan Gidan Gyaran Halin ya bayyana a gaban ta a ranar Litinin ɗin nan da misalin ƙarfe 12:00 na rana, kamar yadda ta umarce shi.

Tunda farko, Mai Shari’a Kurada ya umarci kwanturolan da ya bayyana a gaban kotun ya kuma yi bayanin abinda yasa ya hana likitocin Mista El-zakzaky da matarsa damar duba su a Gidan Gyaran Halin kamar yadda kotun ta bada umarni ranar 6 ga Fabrairu.

Bayan da kotun ta saurari ƙarar ranar 6 ga Fabrairu, sai Mai Shari’a Kurada ya ɗage ƙarar zuwa 24 ga Fabrairu da 25 ga Fabrairu don ba waɗanda ake ƙara su bayyana a kotun don mayar da martani ga ƙarar.

A ranar 6 ga Fabrairun, Babban Lauya, Femi Falana, SAN, ya ce waɗanda ake ƙara sun kasa bayyana a kotun ne saboda “Zeenat, wadda ake ƙara ta biyu kuma matar El-zakzaky ba ta da lafiya, saboda haka waɗanda nake karewa ba su iya zuwa kotu ba”.

An maka Shugaban na IMN da mai ɗakinsa Zeenat a kotu ne bisa zargin su da kisan kai, tara jama’a ba bisa ka’ida ba da kuma tayar da tarzoma da sauransu.

Mai Shari’a Kurada ya amince da roƙon waɗanda ake ƙara na a ba su damar ganin likotocinsu don ba su damar bayyana a kotun a zaman da kotun za ta yi ranar 24 ga Fabrairu da 25 ga Fabrairu.

A zaman kotun na yau Litinin, Marshall Abubakar, wanda shi ma ɗaya ne daga cikin lauyoyin waɗanda ake ƙara ya faɗa wa kotun cewa an hana likitoci damar ganin waɗanda yake karewa, abinda ya saɓa da umarnin kotun.

Kodayake dai Misis Zeenat ta zo kotun, Mista Abubakar ya roƙi kotun da ta gayyaci kwanturolan don ya bada dalilan da suka sa ya bijire wa umarnin kotun.

Kotun ta amince da wannan buƙata, sannan sai aka dakatar da ƙarar zuwa 12:00 don ba kwanturolan damar bayyana a gaban alƙali.

Mista Abubakar ya faɗa wa manema labarai cewa a ci gaba da ƙarar a ranar Litinin da misalin ƙarfe 12:00 na rana, kwanturolan ya bayyana a kotun, ya kuma bada dalilan da suka sa ya hana likotocin ganin waɗanda yake karewa.

Ya ce kotun ta sabunta umarnin ga kotun don ba waɗanda ake ƙara su biyun damar samun dukkan kulawar likitoci da suke buƙata don su iya bayyana a zaman kotun na gaba.

A nasa ɓangaren, Dari Bayero, babban mai shigar da ƙara ya ce kotun ta ba waɗanda ake ƙara cikakkiyar damar ganin likita don kada su ƙara don yanke musu hanzari a zaman kotun na 23 ga Afrilu da 24 ga Afrilu.

Mista Bayero ya ce a shirye suke su gabatar da shaidunsu idan kotun ta dawo zama.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan