Mataimakin Ministan Lafiya Na Iran Ya Kamu Da Coronavirus

66

Kamfanin Dillancin Labarai na ILNA ya bada rahoton cewa Mataimakin Ministan Lafiya na Iran ya kamu da cutar Coronavirus, kamar yadda jaridar Independent ta Birtaniya ta wallafa.

Iraj Harchi ya kamu da wannan cuta da ake kira Covid19, tuni kuma an killace shi, Kakakin Lafiya ta Iran ya bayyana haka a gidan talabijin na gwamnatin ƙasar.

Adadin waɗanda suka kamu da cutar a Iran ya kai mutum 16 a ranar Talatar nan.

A wani labarin kuma, za a killace dukkan fasinjoji 132 da kuma ma’aikata dake cikin wani Jirgin Turkiyya na tsawon kwanaki 14, za a kuma a gwada su a ga ko suna ɗauke da cutar a wani asibiti a Ankara, Ministan Lafiya na Turkiyya ya sanar da haka.

Wannan jirgi yana ɗauke ne da ‘yan Turkiyya da za su dawo gida bayan Ankara ta rufe kan iyakarta da Iran a ƙarshen mako bayan da annobar ta ɓarke a can, Fahrettin Koca ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.

“An tanadi wani jirgi na musamman don ‘yan Turkiyya da suke son dawowa gida daga Iran. Za a killace ‘yan Turkiyya waɗanda suka zo ƙasarmu daga Iran na tsawon kwanaki 14”, in ji Mista Koca.

Turkish broadcaster CNN Turk ta ce ana zargin fasinjoji 17 da suka haɗa da fasinjoji 12 daga yankin Qom na Iran suna ɗauke da wannan cuta.

Wani faifan bidiyo na Kamfanin Dillancin Labarai na Turkiyya, Demiroren, ya nuna motocin asibiti sun yi layi a gefen jirgin bayan ya sauka a Ankara, ga jami’ai da yawa suna sanye da fararen tufafi a inda jirgin ya sauka.

Fiye da mutum 80,000 suka kamu da Coronavirus a China tunda annobar ta ɓarke a ƙarshen shekarar da ta gabata, inda ranar Litinin da ta gabata, adadin waɗanda suka mutu ya kai 2,663.

Cutar dai ta yaɗu a kimanin ƙasashe 29 da yankuna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan