Zamu Ƙara Bunƙasa Tattalin Arziƙin Jihar Kano – Hama Ali Aware

271

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta yi amfani da albarkatun da ke jibge a fadin jihar domin farfado da tattalin arziƙinta.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin mai baiwa gwamna shawara akan harkokin zuba jari daga ƙasashen ƙetare, Hajiya Hama Ali Aware, a lokacin da ta ke ganawa da manema labarai a babban birnin tarayya, Abuja.

Hama Aware ta ƙara da cewa la’akari da yadda Allah ya albarkaci jihar Kano, da damamarkin kasuwanci tare da albarkatun ƙasa, gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ta baiwa maso son juba jari, karfin gwiwa a jihar nan.

“Akwai ɓangarorin masu yawa a fadin jihar nan da masu son su zuba jari za su yi zuba jari, wanda hakan zai amfanar da jihar Kano baki ɗaya. Ɓangarori kamar harkar fatu da kiragu da masana’antu da ma’adanai da kuma harkar noma”

Ta ƙara da cewa gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta mayar da hankali ne wajen ganin ta mayar da jihar Kano jihar da masu zuba jari za su dinga zuwa, wanda hakan zai bunƙasa rayuwar al’ummar jihar.

Hakazalika, Hama Aware ta bayyana cewa noma yana daga cikin abubuwan da jihar Kano ke alfahari da shi, wanda kuma zai ƙara jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen ketare.


A ƙarshe ta ce gwamnatin jihar Kano ta himmatu wajen samar da wani tsari da za a baiwa matasa tallafi, wanda hakan zai ƙara farfado da tattalin arzikin jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan