97

Alkalan wasanni guda 8 ne daga nan gida Najeriya suka tafi kasar Ingila domin samun horo na musamman.

Wadannan alkalan wasa dukkaninsu daga ajin NLO suke wato National League anan gida Najeriya.

Tuni suka fara karbar wannan horo na musamman wanda kuma zasu dauki kamar mako biyu suna karbar wannan horo.

An sanya ranar 6 ga watan Maris domin dawowarsu gida Najeriya dangane da horon da sukaje karbowa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan