Saukar Buhari Daga Karagar Mulkin Ƙasar Ita Ce Mafita Kawai – Sheikh Gumi

677

A lokacin da al’ummar ƙasar nan musamman ma ‘yan yankin arewa suke ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cigaba da zarcewa akan mulki, a ganin da suke shi kadai mutumin da zai iya kai kasar tudun mun tsira.

Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, har yanzu yana nan akan bakan sa na adawa da shugaban kasa Buhari. Yana nan daram akan kalubalantar shugaban kasar duk kuwa da zagin da ‘yan Najeriya suke yi masa akan maganganun da yake kan shugaban kasar.

Duk abubuwan da Sheikh Gumi ya fada a baya akan abinda yake ji a jikin shi game da Buhari da kuma matsalolin da za a samu idan ya karbi mulki duka sun wuce yanzu.

Cikin wata hira da yayi da wakilan jaridar yanar gizo ta DESERT HERALD, Usman Ahmad da kuma Maryam Musa, Malamin ya ce, yayin da Najeriya ke faman fuskantar matsaloli tun kafin yanzu dama shi can hankalinshi bai kwanta da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, kuma shine ya jawo duk abubuwan da suke faruwa a kasar nan yanzu irin su; matsalar tsaro, talauci, rashin aikin yi da kuma kara samun wasu kananan matsaloli na ta’addanci da suka hada da garkuwa da mutane da ta’addanci.

Abinda, Janar Babagana Monguno ya fada a makon da ya gataba, wajen Sheikh Gumi, shine ummul aba’isin da ya sanya aka kasa kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, duk kuwa da alkawuran da ya daukawa al’ummar ƙasar nan.

Sheikh Gumi ya ce ya zama tilas shugaban kasar ya kawo karshen matsalolin da suke damun kasar nan ko kuma ya sauka daga kan kujerarsa baki daya.

“Shawara ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ita ce, ya gane cewa ba shi ne yake da lokaci ba. Ya riga ya bata lokaci mai yawan gaske a baya. Yanzu zance ake yi na abinda zai yiwu, saboda haka yayi amfani da guntun lokacin da ya rage masa wajen kawo karshen wadannan matsaloli da kasar nan ke fuskanta.”

Turawa Abokai

11 Sako

  1. Agaskiya abinda malamin yafada raayinsane kawai amma fa haryanzu babu wanda yakai buhari inganci a mulkin nigeria. Kuma shi wannan malami wata kiyayyace tsakaninsa da buharin sakamakon wani abu da yafaru da babansa marigayi muhammadu gumi shiyasa wannan kiyayyar.kuma yaki yarda yabada kofar cin hanci da rashawa. Wallahi malamin maison zuciyane kuma kasan shugaba buhari bazai yarda da irin wadannan malaman ba.ko yan uwansa malaman izala basa shiri dashi.kawai kiyayyace buharidai yayi maka nisa kuma da buharin irinsane da baiisa yayi irin wannan maganarba,

  2. akullun shuwagabanninmu suna nuna kaunar talakawansu ne abaki amma a aikace babu wata alamar dazata tabbatar dahakan allah shi kyauta

  3. Salon mulkin shugaba muhammadu buhari ba zai haifawa yan Nigeria da mai ido ba, kawai mulkine da jami,an tsaron Nijeria ke cin karensu ba babbaka.Ba Wani jindadi ga talakawa ba.

  4. To gaskiya dai malan , gashi farashi sai ninkawa yake kamar bamuda shuwagabanni Allah ya chanja mana alkàiri

  5. A gaskiya wanda ya rubuta wannan labarin bai nuna kwarewarsa ba. Ku sake duba kalamansa daga farko, ai a matsayinsa na dan jarida bai kamata ya nuna goyon bayansa wa kowa ba.

  6. Agaskiya ina goyon bayan wannan ra’ayi na malam duba da irin rashin kishi da hailn ko in kula da shugaban yake dashi musamman duba da irin tabarbarewar al’amurran kasarnan abunfa yayi yawa ga tsantsagwaron rashin nuna damuwa akan halin da al’umma take ciki

  7. A gaskiya mukam talakawa ba abun da xamuce sai roqon allah ya kawo mana sauqi don wallahi jami’an tsaro suna abun da sukaga dama a wannan mulkin don yanxu hartakai ga akwai farashin rana kuma akwai na dare tunbama mu da muke aikin babbar mota ba a gaskiya akwai gyara a wannan mulkin muna roqon allah ya kawo mana sauki ameen

  8. Allah ya ƙarawa malam lafiya haƙuri da ikhlasi amin ya Allah.
    muna tare da fahimtar ka 100%

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan