Yadda Munich Tayiwa Chelsea Kamun Kazar Kuku

84

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta yiwa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Kamun kazar kuku awasan farko na zagaye na 16 da suka fafata na gasar zakarun nahiyar turai.

Inda Munich din ta lallasa Chelsea daci 3 da nema har birnin London na kasar ta Ingila.

Dukkanin kwallayen an jefa sune bayan an dawo daga hutun rabin lokaci wato mintina 45 na karshe.

Wannan rashin nasara da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tayi yasa anga kamar kungiyar tayi adabo da wannan gasa.

Za a fafata wasa na biyu acan kasar Jamus afilin wasa na Alianz Arena dake birnin Munich.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan