Yawan Shan Barasa Yana Hana Mutuwa Da Wuri – Binciken Masana

189

Wani sakamakon bincike da aka gudanar ya bayyana yawan shan giya zai kai mutum shekaru 90 a duniya.

Sakamakon Binciken ya ƙara da cewa mutumin da ya ke shan giya kwatankwacin kofi daya a rana, ya fi wanda baya sha tabbacin dadewa a duniya da kaso 81.

Hakazalika, mata ma suna da irin wannan damar ta samun dadewa a duniya idan suna dan kurba ruwan na barasa.

Binciken da aka gudanar da shi a Jami’ar Maastrich, da ke kasar Hollanda, ya yi nazari akan adadin mutane 5,500, a tsawon zamani biyu.

Shugaban masu binciken Farfesa Piet van den Brandt, sakamakon bincikenmu ya nuna akwai alaka tsakanin shan giya da kuma tsawon rayuwar mutane maza da mata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan