Coronavirus: Ƙasar Saudiyya Ta Hana Shiga Makkah Da Madina

107

Saudiyya ta sanar da hana maniyatta aikin hajji da umrah shiga biranen Makkah da Madina, a wani matakin hana yaduwar cutar coronavirus mai shafar numfashi.

Ma’aikatar harkokin waje ta Saudiyya ta kuma ce za ta hana shiga kasar ga baki daga kasashen da aka tabbatar akwai cutar ko tana barazana ga kiwon lafiyar al’umma a can.

A sanarwar da ma’aikatar harakokin wajen ta wallafa a Twitter ta kuma ce ta dakatar da amfani da katin shedar dan kasa maimakon fasfo lokacin shiga da fita Saudiyya.

A ranar Laraba Iraqi ta haramta gudanar da ko wane irin nau’in taruka na jama’a, da kuma kulle makarantu da jami’o’in kasar har da wuraren shakatawa saboda fargabar bazuwar a yankin Gabas ta Tsakiya.

A halin yanzu, kasashen Kuwait da Bahrain suma tuni suka dauki irin wadannan matakan, bayan da aka tabbatar da bayyanar cutar ta covid-19 a kasasshen biyu.

Kasashen sun kuma tabbatar da cewa wadanda suka kamu sun shiga kasashen ne daga Iran inda cutar ke habaka fiye da ko ina a wajen China.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan