Yadda Wani Kurtun Soja Ya Kashe Abokan Aikinsa Guda 4 A Borno

108

Rundunar Sojin kasar nan ta ce, wani sojinta da ke aiki a karkashin rundunar da ke yaki da Boko Haram a Malam Fatori na Jihar Barno, ya harbe wasu abokan aikinsa guda 4 har lahira da kuma raunata wasu guda 2 kafin daga bisani ya kashe kansa.

Daraktan Yada Labaran Sojin ƙasar nan, Kanar Sagir Musa ya tabbatar da aukuwar lamarin, yayin da ya ce hukumomin soji na kokarin tuntubar ‘yan uwan wadanda hadarin ya ritsa da su.

Kanar Musa ya ce, tuni aka kaddamar da bincike kan lamarin domin gano dalilin aikata wannan aika-aikar.

Sojin ƙasar nan dai sun kwashe sama da shekaru 10 suna yaki da mayakan Boko Haram wadanda ke amfani da muggan makamai wajen kai hare-hare a birane da kauyukan da ke arewa maso gabashin kasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan