Birnin Da Ya Fi Kowanne Sauƙin Zama A Duniya

235

Birnin Vienna ya kasance wata mahaɗa tsakanin gabashi da yammacin Turai kuma kamfanonin kasashen duniya sun lura da hakan.

A baya-bayan nan ne babban birnin na Austria ya yi wa birane 229 na duniya fintinkau wajen kasancewa birnin da ya fi kowane sauƙin zama, kamar dai yadda wani bincike da kamfanin tuntuba na Mercer, ya yi.

Kusurwar da birnin ya kasance da kuma sauƙin zaman da yake da shi ne suka janyo hankalin ‘yan kasuwa da masu son zuba jari. Manya-manyan gidajen alfarma da zane-zane suna daukar hankalin masu yawon bude.

“Ni a wurina, Vienna ne ya fi kowane birni kyau a Turai,” In ji Magnus Beyer, wani injiniya da ke kwalejin Imperial a birnin London wanda kuma a baya-bayan nan ya je birnin na Vienna domin a manufar kasuwanci, a inda kuma ya halarci babban taron majalisar Turai na kungiyar manazarta kimiyyar Duniya, da aka gudanar a watan Aprilu.

Baya ga sunan da birnin ya yi dangane da yadda ya kasance abin sha’awa tun a zamanin baya, masu ziyarar birnin da aka tambaya sun ce kyawun birnin ne yake jan hankalinsu.

” A koyaushe kyawun birnin ne yake jan hankalinsu. Da yawa daga cikin su suna mamakin yadda mutane suke tafiya a filin Allah ba tare da wata matsala ba da kuma kasancewar ababan na zamani sannan babu cunkoso duk da cewa nan ne babban birnin kasar.” in ji Jan-Paul Dantil, manajan otal na Ritz Carlton da ke Vienna.

Ya kara da cewa mutane daga kasashe da kungiyoyi daban-daban na duniya suna sauka a otal din domin yin kasuwanci.

Jakadun kasashe da manya-manyan jami’an gwamnati da masana suna zuwa nan misali ma shi ne irin mutanen da suka sauka a otal din a lokacin taron Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC. Tun shekarar 1965 kungiyar ta OPEC take gudanar da ayyukanta daga nan Vienna.

Kasancewar Vienna daya daga cikin wurare guda hudu da Majalisar Dinkin Duniya take da ofisoshi a fadin duniya, birnin ya kasance inda wasu daga cikin sassan na MDD suke kamar Hukumar Kula da Makamashi ta MDD. Kuma ofisoshin na MDD suna da ma’aikata 4,400 daga kasashe 120.

Birnin na Vienna wanda yake da yawan jama’a da suka ɗara miliyan 1.8, ya zamo birnin na biyu mafi girma da ake magana da yaren Jamus.

Ursula Kainz na Kungiyar Kasuwanci ta Vienna wadda ke shawartar kamfanoni na cikin gida da na ketare, ya ce akwai dalibai 200,000 da ke jami’o’i daban-daban, abin da ya karawa birnin kimar kasancewa na kowa kuma wanda yake da dimbin matasa da ke more rayuwarsu ta fannin raƙashewa da dare.

“Idan ba ka zo birnin ba shekaru 10 da suka gabata, to yanzu ba za ka iya ɓata, saboda an samu yawaitar gidajen cin binci da mashaya iri-iri da masana’antu sannan kuma akwai kabilu daban-daban.” in ji Kainz.

A baya dai birnin na Vienna ya kasance mahadar Turai ta tsakiya ne kawai amma yanzu birnin ne zuciyar Turai baki daya, tun bayan faduwar Tarayyar Soviet. Kuma alamu na nuna birnin ne kofar bunkasar tattalin arzikin nahiyar Turai daga gabashi.

Bugu da kari, sakamakon kara fadada da Tarayyar Turai ta yi a gabashin nahiyar, Vienna ya zamo wata cibiyar hada-hadar kasuwanci.

Kaninz ya ce fiye da kamfanoni 200 daga kasashe daban-daban da ke da hedikwata a birnin kuma ana samun karin wasu kamfanoni da ke bude ofisoshi.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan