Ƴar Gidan Atiku Abubakar Ta Buɗe Gidan Sayar Da Abinci Bayan Da Kammala Jami’a

195

Walida Atiku Abubakar yar gidan tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, wacce kuma ba ta jima da kammala karatu ba a Jami’ar Amurka a Najeriya da ke Yola. A kwanan nan ne ta yi wani abin mamaki, inda a maimakon a ji ta samu aiki a babbar ma’aikatar gwamnati, sai ta bud’e gidan sayar da abinci mai suna PIESTA RESTAURANT, a kan titin Adetokumbo Ademola Crescent, Abuja.

A lokacin da yake taya ta murna, mahaifinta, Atiku Abubakar ya bayyana a turakarsa ta Twitter cewa, “ina alfahari da hazakarki ta kasuwanci. Lallai kin tabbata abin misali a matsayin shaidar azamar Jami’ar Amurka a Najeriya na koyar da matasa hanyoyin samar da ayyukan yi a kasa.

A kwanakin baya ma an samu labarin yadda diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Hanan, ta kama sana’ar daukar hoto jim kadan da kammala karatunta na jami’a.

Daga Shafin Bashir Malumfashi

Turawa Abokai

2 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan