Hukumar EFCC Ba Ta Da Ikon Kwacemin Kadarorin Da Na Mallaka – Saraki

113

Tsohon shugaban majalisar dattawan kasar nan, Abubakar Bukola Saraki, ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Legas ta yi fatali da bukatar da hukumar EFCC ta kawo gabanta. Bukola Saraki ya bukaci kotu ta yi watsi da karar da EFCC ta kawo inda ta ke bukatar a karbe gidansa da ke Garin Ilorin a jihar Kwara, a mikawa gwamnatin tarayya.

Bukola Saraki ya fadawa kotu cewa bai kamata ta yi amfani da jita-jitar jama’a da ke cewa an gina wadannan gidaje da dukiyar haramun wajen karbe masa dukiyarsa ba.

Lauyan da ya ke tsayawa Abubakar Bukola Saraki watau Kehinde Ogunwumiju SAN, ya roki kotu ta bukaci Jami’an EFCC su kawo hujjar da ke gaskata zargin da ta ke yi.

Babban Lauyan Bukola Saraki Kehinde Ogunwumiju, ya bayyana cewa akwai bukatar hukumar EFCC ta fito da hujja mai gamsarwa kafin a damka mata gidajen har abada.

Lauyan da ke kare tsohon gwamnan Kwara, ya fadawa Alkali mai shari’a Rilwan Aikawa cewa EFCC ba su kawo wata hujjar da za ta sa a mallaka masu gidajen ba.

A cikin watan Disambar shekarar 2019, EFCC ta samu iznin kotu na karbe wasu gidajen Bukola Saraki da ke Unguwar GRA a Garin Ilorin, da zargin cewa da kudin sata aka gina gidajen.

Haka zalika Saraki ya yi magana ta bakin Mai magana da yawunsa, Yusuph Olaniyonu, wanda ya bayyana cewa ba a filin gwamnati aka gina wadannan gidaje ba.

A cewar EFCC, Saraki ya saci Biliyan 10 daga asusun Kwara a lokacin ya na gwamna, wanda ta ce da wannan kudi aka gina gidajen. Tuni ya karyata wannan zargi

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan