Jam’iyyar APC Za Ta Gurfanar Da Gwamnan Taraba A Gaban Kuliya

111

Babbar jam’iyyar hamayya ta APC a jihar Taraba ta sha alwashin gurfanar da gwamnan jihar a gaban kotu idan bai miki mulki ga mataimakinsa ba.

Shugaban jam’iyyar ta APC, Ibrahim Elsudi ya ce sun bai wa Gwamna Darius Ishaku wa’adin mako guda ya mika mulki hannun mataimakinsa ko kuma su hadu a kotu.

APC na zargin gwamnan da kwashe fiye da tsawon wata biyu ba ya zaune a jihar, abin da ta ce ya zarce wa’adin da tsarin mukin kasar ya ba shi.

Sai dai bangaren gwamnan jihar ya yi watsi da wannan barazana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan