Jihar Sokoto Za Ta Maye Tsarin Almajiranci Da Fasalin Karatun Ƙasar Indonesia

338

Gwamnatin jihar Sokoto tace tana tunanin kawo tsarin karatun kasar Indonesia wanda aka fi sani da Pondok Pesantren Madrasah, domin maye gurbin karatun allo a jihar Sokoto.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal shine ya bayyana haka a jiya Lahadi a lokacin da ya gana da jakadan kasar Indonesia a kasar nan, AVM Usra Hendra Harahap, wanda ya kai masa ziyara jihar Sokoto.

Sai dai kuma gwamnan yace gwamnatinsa ba wai tana gaggawa bane wajen dakatar da harkar Almajirancin ba tare da ta kawo wata hanya da za ta maye gurbin tsarin ba.

Wannan dai yazo ne a sanarwar da aka bawa manema labarai a jihar ta Sokoto wanda mataimakin gwamnan a fannin sadarwa Muhammad Bello ya bada.

Ya ce tsarin Pondok na amfani da Masallatai, kananan makarantu, inda shugabannin addini suke amfani da su wajen koyar da addinin Musulunci.

Haka kuma Tambuwal ya ce gwamnatinsa za ta tuntubi Sarkin Musulmai Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da kuma sauran masu fada aji na jihar domin jin ta bakin su akan wannan sabon tsari.

Da yake bayyana jin dadin shi ga gwamnatin kasar ta Indonesia, Tambuwal ya bayyanawa jakadan cewa ziyarar shi za ta kawo kwakkwarar alaka tsakanin jihar da kasar ta Indonesia.

Ya ce tuni jihar ta riga tana kokarin kawo cigaba a fannin lafiya, tattalin arziki da kuma kasuwanci ta fannin addinin Musulunci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan