Rashin Wayewar Mata Ne Silar Yawan Mutuwar Aure – Anti Bilki

240

Fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, Bilkisu Funtua ta bayyana rashin wayewa da karancin ilimi daga bangaren mata a dalilan da ke jawo mace-macen aure a arewacin kasar nan.


Fittaciyar marubuciyar ta bayyana hakan ne a wata hirar da ta yi da sashen Hausa na BBC.


Marubuciyar wadda aka fi sani da Anti Bilki ta ce ta fara rubutu ne domin samar da mafita ga matsalolin mutuwar aure a arewacin kasar nan.


Duk da cewa babu alkaluma a hukumance, amma an yi kiyasin cewa arewacin kasar nan ne yankin da yafi kowanne yanki a Afirka ta yamma yawan mutuwar aure.


Marubuciyar, wacce littafinta na farko shi ne “Allura Cikin Ruwa”, ta nuna takaicinta ga irin halin da ‘ya mace ta sami kanta a kasar Hausa.


Anty Bilki ta ce a baya-bayan nan na ji Hajiya Naja’atu na fadar wani abu da ta taba ji daga bakin Malam Aminu Kano inda yake cewa, “Ita ‘yar Bahaushiya ba ta aje komai ba, sai dai a yi mata aure, ta ci abinci, ta haihu, ta mutu, shi ke nan an kashe rayuwar yarinya Bahausa.”

A ganinta, samar da ilimin addini da na zamani su ne mafita wajen rage aukuwar mutuwar aure a tsakanin al’ummomin arewacin kasar nan.

Ta kara da cewa idan dai aka ilimintar da ‘ya mace to hakika za a samu raguwar samun sabani a gaidajen aure ta bangaren abin rufin asiri da tarbiyyar yara.


“Idan yarinya na da ilimi ko ba ta yi aiki ba to za ta samu dabarun tsayawa da kafafunta da neman na kai da rage dogaro da miji.


“Za kuma ta zamo uwa ta gari da za ta haifi ‘ya’yan da al’umma za ta yi alfahari da su.”

Ta ce an kai lokacin da ya kamata al’ummar arewacin kasar nan su tashi tsaye don ganin an rage samun wannan matsalar, kamar yadda ba a cika samu ba a Kudancin kasar nan ba.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan