An Taɓa Hanani Aure Akan Zargin Neman Maza — Adam Zango

75

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Adam Zango ya ce a kullum yana kwana yana tashi da bakin cikin zargin da wasu suke yi masa na neman maza.


Hakan ne ya sa jarumin daukar Al’kur’ani ya rantse cewa bai taba neman wani namiji ba da lalata.


“Wannan abun yana hana ni barci, kai har ma na taba zuwa neman aure amma aka hana ni saboda haka.” In ji Zango.

Wasu dai musamman masoya na zargin Adam Zango da girman kai.


To amma jarumin ya ce “idan kana maganar masoya kana maganar miliyoyin mutane to ta ya ya zan gamsar da su?


Zango ya nemi masoyan nasa da su rinka yi masa uzuri domin shi ma mutum ne kamar kowa.


Ya kuma nanata maganar da ake alakanta wa ga masu wasan fina-finan Hausa cewa “kudi suke nema”, a inda ya ce “muna yin fina-finan da za su kawo mana kudi.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan