Saudiyya Ta Sanar Da Ɓullar Coronavirus A Ƙasar

98

Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da ɓullar Coronavirus karon farko a ƙasar.

A cewar wani rahoto da jaridar Saudi Gazette ta fitar, an samu ɓullar cutar ne ta hanyar wani ɗan Saudiyya wanda ya dawo daga Iran, inda ya biyo ta Bahrain.

Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya ta ce a halin yanzu tana killace da wannan mutum, ta kuma ce ta ɗebo jinin dukkan mutanen da mara lafiyar ya yi mu’amala da su don yin gwaji.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 27 ga Fabrairu, Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Ƙetare ta Saudiyya ta sanar da dakatar da zuwa Umara sakamakon tsoran bazuwar Coronavirus.

Ma’aikatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan bibiyar yadda Coronavirus, wadda aka sauya wa suna zuwa Covid19 ke yaɗuwa a ƙasashen duniya.

Saudiyya ta kuma dakatar da ‘yan ƙasashen Yankin Gulf GCC, shiga birane biyu masu tsarki na Maka da Madina bisa tsoron Coronavirus.

A cewar majiyarmu, GCC wata ƙungiya ce ta ƙawancen ƙasashen Gabas ta Tsakiya su shida da suka haɗa da Saudiyya, Kuwait, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Qatar, Bahrain da Oman, an kuma kafa wannan ƙungiya ne a babban birnin Saudiyya, wato Riyadh a watan Mayu, 1981.

Saudi Gazette ta kuma jiyo Ma’aikatar Lafiyar na cewa wannan hani bai shafi ‘yan ƙasashen na GCC ba waɗanda suke zaune a Saudiyya kuma ba su nuna alamun kamuwa da Coronavirus ba tsawon kwana 14, kuma za ma su iya neman izinin yin Umara daga Ma’aikatar Aikin Haji.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan