Tsohon shugaban INEC Maurice Iwu Ya Ce Ya Gano Maganin Coronavirus

123

Maurice Iwu ya nemi gwamnati ta dauki nauyin tawagarsa domin samar da kwayoyin maganin cutar da yawa.
Kafafen watsa labarai a kasar nan sun ambato tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa, INEC, Farfesa Maurice Iwu yana ikirarin samo maganin cutar numfashi ta Covid-19, ko kuma coronavirus.

Ya zuwa wannan lokaci, cutar ta kashe fiye da mutum 3,000 a fadin duniya, inda kuma kasarsa Najeriya ta kasance cikin kasashen da cutar ta bulla.

Tun da cutar ta bulla a China shekarar da ta wuce, babu wani maganin ta da aka amince da shi. Kazalika ba a sa ran samun maganin ta sai nan da tsakiyar shekara mai zuwa, domin kuwa masu bincike a Amurka suna can suna gwajin maganin na coronavirus a kan dabbobi.

Amma ranar Litinin Farfesa Maurice Iwu, wanda ke shugabantar cibiyar bincike ta Bio-Resources Institute of Nigeria, ya gana da ministan lafiya da na kimiyya domin neman tallafinsu kan maganin da ya ce ya gano, a cewar jaridar Vanguard

An ambato Farfesa Iwu, wanda yanzu haka yake fuskantar tuhuma kan zargin halasta kudin haramun a wata kotun Najeriya yana cewa tawagarsa ta masu bincike “ta gano maganin Covid-19 a shekarar 2015”.

Yana so gwamnati ta dauki nauyin tawagarsa domin samar da kwayoyin maganin cutar da dama.

Jaridar intanet ta Sahara Reporters ta ambato ministan Kimiyya da Fahasa, Mohamed Abdullahi, yana cewa sun aike da abubuwan da aka hada maganin ga wani kwamiti na musamman na Cibiyar Kimiyya ta Najeriya domin tantance su.

“A wani bangare na tattaunawar da ake kan Coronavirus (Covid-19), Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha ta karbi bakuncin Farfesa Maurice Iwu, wanda ya shaida mana cewa ya samo maganin da ka iya warkar da Covid-19.

“Ma’aikatar Kimiyya da Fahasa ta mika wannan magani ga kwamiti na musamman na Cibiyar Kimiyya ta Najeriya domin tantance su. Shugaban Cibiyar zai jagoranci sauran masana domin gano gaskiyar wannan ikirari,” in ji shi.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan