Wani Asibiti Na Amfani Da Jannareto 75 Saboda Rashin Wuta

144

University College Hospital, UCH dake Ibadan yana amfani da jannareta har guda 75 don aiwatar da aikace-aikacensa na duba lafiya, a cewar hukumar gudanarwar asibitin.

Shugaban Asibitin, Jesse Otegbayo ya bayyana haka ranar Litinin a taron cikarsa shekara ɗaya a ofis, a cewar rahoton jaridar The Punch.

Ya ce rashin tsayayyiyar wutar lantarki ya sauya ingancin aikin asibitin ta fuskar bincike, horo da kula da marasa lafiya.

Mista Otegbayo ya ce rashin wutar lantarki shi ne babban ƙalubalen da yake fuskantar asibitin.

“Zan iya cewa manyan ƙalubale guda uku da muke fuskanta a UCH su ne wutar lantarki, wutar lantarki da haske.

“Zai ba ku sha’awa ku lura da cewa muna da kusan jannareta 75 a wurare daban-daban a harabar asibitin.
“A taƙaice, mukan samu miliyan N200 duk wata. Kada a kalli wannan shi kaɗai. Za ku so ku tambaya nawa muke kashewa wajen siyan mai, siya da gyaran jannareta da sauran buƙatu.
“Ina son in ce wannan jimla ta yi kaɗan. An yi sa’a, muna da mutane na gari waɗanda ke kawo taimako don mayar da abinda muke kashewa.
“Babban ƙalubale da yake fuskantar mu, shi ne wutar lantarki. Nan asibiti ne, ba sai an faɗi amfanin samun tsayayyiyar wutar lantarki ba. Yi tunani, a ce ana yi wa mara lafiya aiki sai a ɗauke wuta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan