Yadda Wuta Ta Kama Motar Lobi Stars Suna Cikin Tafiya

117

Ayayin da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Lobi Stars suke rusa gudu akan hanyarsu ta komawa birnin Makurdi kwatsam suka gamu da wani mummunan hadari na motarsu ta kama da wuta.

Saidai ganin yadda motar ta kama da wuta ‘yan wasan kungiyar kwallon kafan ta Lobi tare da direbobin suka dinga fasa gilashi suna tsalle suna fitowa daga motar.

Rahotanni sun bayyana cewar babu dan wasa ko direban dayarasa ransa amma kayayykin ‘yan wasan tare da motar sun kone kurmus.

Jaridar Labarai24 ta tattauna da wani maisuna Samuel inda ya halacci wajen kuma ya bayyana mana cewa “lokacin danaje wajen na taras wuta tanacin motar kuma ‘yan wasa suna ta kururuwa da ihu akawomusu dauki, saidai ni banga wanda ya mutu ba amma naga wasu sunji rauni da dama”

Lobi Stars dai sun dawo daga buga gasar cin kofin ajin Firimiya ta kasar nan wasan mako na 22 wannan tsautsayi ya afkamusu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan