Yawan Adadin Makafi Zai Ƙaru A Duniya — Bincike

176

Wani sabon bincike ya nuna cewa yawan adadin masu makanta a fadin duniya zai linka har sau uku a cikin shekaru masu zuwa.


Binciken wanda aka wallafa a wata mujallar kiwon lafiya ta Lancet (Global Health) , ya yi hasashen cewa matsalar za ta karu daga adadin miliyan 36 da ake da shi a yanzu, zuwa miliyan 115 nan da shekara ta 2050, muddin ba a inganta hanyoyin magancewa ba.


Masu binciken sun ce fafutikar da ake yi kan adadin yawan al’ummar duniya na matsalolin idanun na kara gamuwa da cikas a cikin shekarun baya-bayan nan.


Yankunan da matsalar ta fi kamari sune kudanci da gabashin Asia, yayin da yankunan kudu da saharar Afirka suma suke da adadi mai yawa.


Binciken dai ya yi kira ga a samu ingantuwar hanyar magance matsalar, ta hanyar saka kudi a fannin aikin tiyatar cutar yanar ido da makamantansu, da kuma samar da madubin idanun ga mutanen da ke da bukata.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan