Zargin Cin Hanci A Ma’aikatar Tsaro: Kwankwaso Ya Wanke Kansa Da Ganduje

147

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya nesanta kansa da hadimansa daga zargin da ake musu na shiga cikin wata badaƙala lokacin da yake Ministan Tsaron Najeriya.

A cewar rahotannin wasu jaridu, a ranar Litinin ne Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC ta ƙaddamar da bincike a wasu kwangiloli a Ma’aikatar Tsaro a 2008.

Sai dai Mista Kwankwaso ya riƙe muƙamin Ministan Tsaro ne daga 2003 zuwa 2006.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Kwankwaso, PPS, Mudathir Inuwa Muhammad ya fitar, tsohon ministan ya ƙaryata waɗannan rahotonni, yana mai cewa ba shi ne minista ba a lokacin da aka bayar da waccan kwangila da ake magana.

“Bai ma kamata mu damu mu mayar da martani ga rahotannin jaridu da na soshiyal midiya ba marasa tushe dake yawo dake da nufin ɓata sunan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso; amma sakamakon ganin wasu kafafen watsa labarai masu inganci suna yaɗa waɗannan rahotonni hakan ya tilasta mu mayar da martani.

“Zargin cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da mataimakansa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje (gwamnan jihar Kano mai ci) wanda yake Mataimaki na Musamman ga Sanata Kwankwaso a Ma’aikatar Tsaro da Abba Yusuf (wanda shi ma yake Mataimaki na Musamman ga Sanata Kwankwaso a dai Ma’aikatar ta Tsaro) ana binciken su bisa zargin almundahana wajen bayar da kwangila a Ma’aikatar Tsaro ta Ƙasa abu ne na yaudara kuma ba gaskiya ba ne. Ɗaya daga cikin kafafen watsa labaran ma ta yi zargin cewa Abba Yusuf da Dr. Abdullahi Umar Ganduje sun karɓi miliyan 30 da miliyan 50 kowannesu. Wannan ma ba gaskiya ba ne.

“Muna son mu ajiye bayanai yadda suke mu kuma jawo hankalin al’umma gaba ɗaya cewa a wancan lokaci da ake zargin an bada kwangilar da ake zargi, wato 2007, Sanata Kwankwaso ba shi ne Ministan Tsaro ba.

“Ya ajiye muƙamin Ministan Tsaro a watan Nuwamba, 2006 don ba kansa ‘yancin yin takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP. Maganar gaskiya, muƙamin da yake riƙe da shi a lokacin shi ne yana wakiltar Arewa Maso Yamma a Hukumar Bunƙasa Yankin Naija Delta, NDDC. Muƙamin da shi ma ya ajiye bisa raɗin kansa a 2010 saboda rashin gamsuwarsa da yadda ake ayyuka na cin hanci a yadda ake tafiyar da hukumar.

“A wancan lokaci, Dr. Ganduje yana Ndjamena a matsayin Babban Sakataren Hukumar Kula da Tafkin Cadi. Saboda haka, ba yadda za a ce a wancan lokaci an samu Sanata Kwankwaso ko wasu daga cikin mataimakansa da hannu a cikin wata badaƙalar ma’aikatar tsaro.

“Saboda haka muna jawo hankalin dukkan kafafen watsa labarai masu daraja musamman jaridu da su guji wallafa irin waɗannan labarai marasa tushe waɗanda ba kawai za su zubar da kimar ɗaiɗaikun mutane masu daraja ba, amma har da su kansu kafafen watsa labaran”, in ji sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan