Hukumar Yaƙi Da Rashawa A Jihar Kano Ta Buƙaci Sarki Sanusi Ya Bayyana A Gabanta

94

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafen al’umma ta Kano ta fara wani sabon bincike kan zargin karkatar da kudade da ake yi wa Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi II.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa hukumar ta aike da takardar gayyata ga Sarkin na Kano a yau Laraba.

Hukumar dai tana bukatar Sarkin ya bayyana a gabanta gobe Alhamis domin amsa tambayoyi kan yadda aka sayar da wasu filaye mallakin masarautar aka kuma karkatar da wasu miliyoyi naira.

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce an gayyaci Sarkin ne bayan tambayoyi ga daya daga manyan ‘yan majalisarsa, wanda ake zargi yana da hannu a badakalar karkatar da kudaden.

Hukumar ta karbar korafe-korafe ta kaddamar da bincike da dama kan masarautar Kano karkashin Sarki Muhammadu Sanusi II da kuma shi kansa Sarkin.

Binciken da hukumar ta yi sun hadar da na zargin yadda aka kashe wasu daruruwan miliyoyi naira wajen biyan kudin waya tun bayan hawan Sarkin Muhammadu Sanusi II karagar mulki, da bincike kan zargin yadda ake sayar da wasu filaye na gandun Sarki ba bisa ka’ida ba, da kuma bincike kan zargin sayar da filayen masarauta a unguwar Darmanawa da karkatar da kudin.

Ita dai masarautar Kano da Sarki Sanusi II sun sha musanta duk zarge-zargen.

Wasu dai na ganin duka binciken da majalisar da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi na da nasaba da siyasa musamman ganin rashin jituwar da ke tsakanin Sarkin na Kano da Gwamna Ganduje.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan