Kuɗaɗe Na Iya Yaɗa Cutar Coronavirus – Hukumar Lafiya Ta Duniya

23

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar kudade na taimakawa wajen bazuwar coronavirus.

Mai magana da yawun hukumar ya bayar da shawara ga jama’a da su rinka amfani da hanyoyin zamani wajen biyan kudi domin rage yiwuwar yaduwar cutar.

“Mun san cewa ana musayar kudi tsakanin mutane kuma kudade na dauke da kwayoyin cuta,” in ji mai magana da yawun hukumar.

A watan da ya gabata ne China da Korea suka fara yin feshi ga kudade da killace su domin rage yaduwar cutar coronavirus.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan