Majalisa Za Ta Binciki Sarkin Kano Sanusi II Akan Furta Kalmomin Da Ba Su Dace Ba

132

Majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagaorancin Abdulaziz Garba Gafasa, ta karbi korafi akan Mai Martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II a zaman majalisar na yau.

Tun da farko wasu mutane biyu ne su ka gabatar da korafi akan Sarki Sanusi II, bisa zargin furta kalmomin da ba su dace ba akan addini da kuma al’ada.

Bayan gabatar da korafin da dan majalisa mai wakilta karamar hukumar Sumaila, Zubairu Hamza, majalisar ta kafa kwamiti domin ya duba wannan korafi ya kuma bata rahoto cikin kwana 7.

Idan za a iya tunawa dai an samu tsamin dangantaka tsakanin gwamnatin jihar Kano da kuma masarautar Kano, wanda hakan ya haifar da dokar da ta samar da masarautun Rano da Bichi da Karaye da kuma Gaya.

Bayan kammala zabukan shekarar 2019, aka fara samun takun-saka tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi, lamarin da ya yi kamarin da ba a taba zaton zai yi ba.

Gwamna Abdullahi Ganduje da magoya bayansa suna zargin Sarki Sanusi da goyon bayan dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna.

Sun yi zargin cewa ya fito fili ya yaki Ganduje, kuma ya yi amfani da kudinsa wajen yi wa dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP yakin neman zabe, sai dai sarkin ya musanta wannan zargi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan