Mun Ga Alkhairin Rufe Iyakokin Ƙasar Nan – Buhari

94

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta aiki da shawarar wani kwamitin bangare uku da ya kunshi Nijeriya da Benin da Jamhuriyar Nijar game da tsuke iyakokin k’asar na tudu da gwamnatinsa ta yi.

Ya ce da zarar kwamitin ya kammala aikinsa kuma ya mika wa kasar nan rahoto, gwamnatinsa za ta duba wannan batu.

Babban mataimaki na musamman kan harkar yada labarai na shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fadawa BBC cewa gwamnati na dakon abinda rahoton zai gabatar kafin daukar mataki na gaba.

A cewarsa akwai miyagun halaye da ake gudanarwa ta anfani da makwabtan kasashen da suka hada da fasakwauri da kuma safarar miyagun kwayoyi da makamai.

A cewar Malan Garba Shehu matsawar aka kiyaye dokokin da Najeriya zata shimfida to abu ne mai sauki a iya bude kan iyakar, to amma ya ce ga yanzu babu wannan magana a kasa.

Mai bada shawarar ya ce Najeriya ta ga dimbin alfanun da ke akwai a dalilin rufe kan iyakokin, la’akari da alkhairan da yan kasar suka samu musamman manoman shinkafa.

Ya ce abun alfahari ne ganin yadda yan kasar suka fahimci cewa za su iya noma abincin da za su ci har su sayar cikin sauki.

Sama da wata shida ke nan da gwamnatin Nijeriya ta rufe iyakokinta da nufin shawo kan matsalar fasa-kwaurin shinkafa da sauran haramtattun kayayyaki.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan