Takardun Kuɗi Na Bankuna Ka Iya Yaɗa Coronavirus-WHO

125

Takardun kuɗi na bankuna ka iya yaɗa sabuwar cutar Coronavirus, wadda aka sauya wa suna zuwa Covid19, saboda haka ya kamata mutane su riƙa amfani da tsarin biyan kuɗi na Intanet, a cewar Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, WHO.

Ya kamata kwastomomi su riƙa wanke hannayensu bayan taɓa takardun kuɗi na bankuna, domin kuwa Covid19 mai saurin yaɗuwa ka iya maƙalewa a kan takardar kuɗi tsawon kwanaki, Hukumar Lafiyar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana haka ranar Litinin.

Don kare yaɗuwar cutar, ya kamata mutane su riƙa amfani da fasahar biyan kuɗi na Intanet, a inda hakan zai yiwu, a cewar wani kakakin WHO.

Bankin Ingila ya amince cewa takardun kuɗi na bankuna “ka iya ɗaukar ƙwayar bakteriya”, sannan ya yi kira ga jama’a da su riƙa wanke hannayensu a kai a kai.

Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan China da Korea sun fara zuba magani a kan takardun kuɗi na bankuna da aka yi amfani da su, tare da killace su a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinsu wajen rage yaɗuwar cutar.

Majiya: The Telegraph UK

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan